Canjin sheka: Gwamnan PDP ya gana da tsohon gwamnan jam’iyyar da ya koma APC, hotuna

Canjin sheka: Gwamnan PDP ya gana da tsohon gwamnan jam’iyyar da ya koma APC, hotuna

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma sanata mai ci, Godswill Akpabio, wanda ya koma jam’iyyar APC a watan nan, ya gana da gwamnan jihar Enugu, Ifeayi Ugwuanyi.

An yi ganawar ne a fadar gwamnatin jihar Enugu, sai dai ba a bayyana abinda suka tattauna ba yayin ganawar.

Bayan ganawar ta su, Akpabio, ya bayyana a shafinsa na Tuwita cewar yana godiya ga gwamna Ugwuanyi tare da mutanen jihar Enugu bisa goyon bayan da suka nuna masa.

Canjin sheka: Gwamnan PDP ya gana da tsohon gwamnan jam’iyyar da ya koma APC, hotuna

Akpabio da gwamna Ugwuanyi

Canjin sheka: Gwamnan PDP ya gana da tsohon gwamnan jam’iyyar da ya koma APC, hotuna

Ugwuanyi da Akpabio

Bayan komawar sa jam’iyyar APC, Akpabio, ya yi alkawarin zai tabbatar cewar shugaba Buhari ya samu kuri’u mafiya rinjaye daga yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani katafaren aiki a filin jirgin Abuja, (Hotuna)

Ko a kwanakin baya saida jam’iyyar APC, ta bkin gwamna Rochas na jihar Imo, ta bayyana cewar akwai kimanin gwamnonin PDP 5 dake yi masu aiki ta karkashin kasa domin samun nasarar lashe zaben shugaban kasa a zaben 2019.

Canjin sheka: Gwamnan PDP ya gana da tsohon gwamnan jam’iyyar da ya koma APC, hotuna

Gwamnan PDP ya gana da tsohon gwamnan jam’iyyar da ya koma APC

Canjin sheka: Gwamnan PDP ya gana da tsohon gwamnan jam’iyyar da ya koma APC, hotuna

Gwamnan PDP ya gana da tsohon gwamnan jam’iyyar da ya koma APC

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel