Dakarun soji sun yi nasarar kwato kananan yara 23 daga hannun kungiyar Boko Haram

Dakarun soji sun yi nasarar kwato kananan yara 23 daga hannun kungiyar Boko Haram

Hukumar Sojin Najeriya ta mika kananan yara 23 data ceto daga hannun Boko Haram da jami'an Asusun yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin a basu kullawa na musamman kafin a mayar dasu hannun iyayensu su cigaba da rayuwa cikin jama'a.

Kwamandan Operation Lafiya dake aikin samar da tsaro a Arewa maso gabas, Manjo Janar Abbah Dikko ne ya bayar da wannan sanarwan a hedkwatan hukumar dake Maiduguri inda yace sunyi hakan ne domin haka ka'idar take a dukkan kasashen duniya.

Dikko ya ce, "Kamar yadda dokar aikin soji na duniya ta tanada, mun mika wadannan yaran da suka dade hannun mayakan kungiyar ta'addan Boko Haram ga kungiyar UNICEF.

Dakarun soji sun yi nasarar kwato kananan yara 23 daga hannun kungiyar Boko Haram

Dakarun soji sun yi nasarar kwato kananan yara 23 daga hannun kungiyar Boko Haram

A jawabinsa, Mr Geoffrey Ijumba na ofishin UNICEF da ke jihar Borno ya yi maraba da yaran wanda shekarunsu ke tsakanin 12 zuwa 17.

KU KARANTA: 2019: El-Rufa'i ya gargadi jam'iyyar APC

Ya ce UNICEF na aiki tare da Hukumar Sojin Najeriya da Ma'aikatan Harkokin Mata na jihar Borno domin samar da bayar da magani ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa da basu kulawa ta musamman.

Ya ce, "Daga yau zamu fara bawa yaran nan kulawa ta musamman domin ganin cewa nan da wani lokaci zasu iya komawa wajen iyalensu domin cigaba da rayuwa cikin jama'a.

Pernille Ironside, wakilin UNICEF na wucin gadi, ta jadada cewa UNICEF zata cigaba da aiki tare da Hukumar Sojin Najeriya da sauran hukumomi domin taimakawa dukkan yaran da aka ceto daga hannun Boko Haram.

Ironside ta kara bayyana muhimmancin bawa yaran gudunmawa domin su cimma burin da suka sanya gaba a rayuwa inda tace hukumar ba zata yi kasa a gwiwa ba har sai taga dukkan yaran sun koma gida wajen iyalensu kamar yadda NAN ta wallafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel