Dalilin da yasa ba zamu daga zaben 2019 - INEC

Dalilin da yasa ba zamu daga zaben 2019 - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tace ba zata dage babban zaben shekarar 2019 ba kawai saboda an samu jinkiri wajen amincewa da kasafin kudin hukumar.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai daga gidan gwamnati a ranar Juma'a a Abuja.

Ya ce babu kudin tsarin mulki bai bayar da ikon dage zaben ba saboda haka ba zai yiwu a dage zaben ba.

Dalilin da yasa baza mu iya daga zabe ba - INEC

Dalilin da yasa baza mu iya daga zabe ba - INEC

"Kamar yadda na saba maimaitawa, babu wani dalili da zai hana a gudanar da zabe a cikin dokar zabe na kasa mai lamba 26 dake kundin tsarin mulki.

"Mun tsayar da ranar zaben, za'a fara a ranar 16 ga watan Fabrairun 2019; mun fitar da jadawalin zaben kafin zaben yazo, wannan shine karo na farko da hakan ta faru a tarihin Najeriya. Jama'a sun san lokacin da za'a fara zaben shekara daya kafin fara zaben."

DUBA WANNAN: 2019: El-Rufa'i ya gargadi jam'iyyar APC

Ya cigaba da cewa, "A karo na farko, jama'a sun san nawa ne hukumar zabe zata kashe wajen gudanar da zaben, mutanen sun san didigin yadda hukumar ta gabatar da kasafin kudin ta da yadda za'a kashe kudin.

"Ina farin ciki kuma na gamsu da yadda lamarin ke tafiya."

Yace hukumar ta kara budde sabbin rumfunan rajistan zabe amma dole za'a dakatar da gudanar da rajistan zaben kamar yadda doka ta tanada cewa a dakatar da rajistan watanni shida kafin fara zaben.

Sai dai saboda kiraye-kirayen da 'yan Najeriya su kayi, INEC ta kara wa'addin rajistan zaben zuwa karshen watan Augusta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel