Za mu yi nasarar lashe Kujerar Gwamnan jihar Osun - ADP

Za mu yi nasarar lashe Kujerar Gwamnan jihar Osun - ADP

A ranar Asabar din yau ne jam'iyyar ADP watau Action Democratic Party, ta bayyana tabbaci gami da amincewar ta na yin fatali da jam'iyyar APC yayin zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar a ranar 22 ga watan Satumba.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Mista Yabagi Sanni, shine ya bayyana wannan aminci yayin ganawa da masu ruwa da tsakin jam'iyyar na yankin Kudu maso Yammacin kasar nan a jihar Legas.

Yake cewa, tuni akayi walkiya domin kuwa al'ummar jihar Osun sun bayyana karara irin kosawar da mulkin jam'iyyar APC inda a halin yanzu suke neman jam'iyyar ta ADP ta kawo ma su dauki.

A sanadiyar haka ya sanya a kwana-kwanan nan al'umma da dama ke ci gaba da tumbatsa da cincirindon shiga jam'iyyar da hakan ke inganta karfafuwar yayin da zaben gwamnan jihar ke gabatowa.

Za mu yi nasarar lashe Kujerar Gwamnan jihar Osun - ADP

Za mu yi nasarar lashe Kujerar Gwamnan jihar Osun - ADP

Rahotanni sun bayyana cewa, Alhaji Moshood Adeoti, shine mashahurin dan takara na jam'iyyar ta ADP, wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa ADP kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar karkashin jagoranci gwamna Rauf Aregbesola.

Shugaban jam'iyyar ya ci gaba da cewa, gwamnatin APC ta gaza ta fuskar kowane mataki wajen sauke nauyin da rataya a wuyan ta na samar da ci gaban kasa da ingantawa al'ummar kasar nan.

KARANTA KUMA: Mahaifar Shugaba Buhari ta shirya tsaf domin isowar sa

A sanadiyar sabanin ra'ayoyi Legit.ng ta fahimci cewa, jam'iyyar ta ADP ta yi hannun riga da kungiyar jam'iyyun nan da ta hada kai domin kalubalantar jam'iyyar APC a zaben 2019.

Mista Sanni ya kuma yi tir gami da Allah wadai dangane da takaddamar majalisar dokoki ta tarayya da ya bayyana cewa mambobin ta na kai ruwa rana ne a tsakanin su domin cimma manufofi na soyuwar zukatan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a zaurukan sada zumunta kamar haka:

https://www.business.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel