Shugaba Buhari ya yi ta'aziyyar rashin Kofi Annan

Shugaba Buhari ya yi ta'aziyyar rashin Kofi Annan

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga jama'a da gwamnatin kasar Ghana bisa rasuwar tsohon sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Kofi Annan wanda ya rasu a safiyar yau 18 ga watan Augustan 2018.

Shugaba Buhari ya kira shugaba Nana Akufo-Addo daga Landan inda ya yi masa jaje kana ya fada masa cewa dukkan 'yan Najeriya da kasashen ECOWAS za suyi rashin marigayin musamman idan a kayi la'akari da irin rawar da yake takawa wajen daura nahiyar Afirka kan turbar cigaba.

Shugaba Buhari ya yi ta'aziyya game da rasuwar Kofi Annan

Shugaba Buhari ya yi ta'aziyya game da rasuwar Kofi Annan

Kofi Annan shine dan Afirka na farko da ya taba shugabantar majalisar dinkin duniya kuma dan Afirka na farko da ya lashe lambar karramawa na Nobel tare da majalisar dinkin duniya.

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

Shugaba Buhari yace duk da cewa Annan dan Ghana ne, ayyukansa na alkhairi da iya shugabanci da taimakon al'umma da ya yi zasu kasance a zukatan jama'a. Ya kuma ce duniya ba za ta taba mantawa da gudunmawar da marigayin ya bayar wajen yaki da cutar Kanjamau.

Shugaba Buhari kuma ya aike ta ta'aziyya ga matar marigayin, Nane Maria Annan da sauran iyalensa da ma'aikatan majalisar dinkin diuniya da sauran kungiyoyi da yake shugabanci kamar kungiyar Elders da marigayi shugaban kasa Nelson Mandela ya kafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel