Zamu tsige Saraki ko ta wane hali - Omo Agege

Zamu tsige Saraki ko ta wane hali - Omo Agege

Wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress APC, kuma dan a mutun shugaba Muhammadu Buhari, Sanata Ovie Omo-Agege, ya sanar da cewa kusoshin jam'iyyar APC suna dawowa wuraren su a majalisar tarayya.

Sannan Sanatan ya bayyana cewa kusoshin jam'iyyar APC, ba zasu amince da kudurin da aka kawo na hadin kai tsakanin majalisar dattawa da majalisar wakilai, domin suyi aiki tare ba, kamar yanda Saraki da Dogara suka bukaci hakan.

A lokacin da Sanatan yake magana da wakilin, ya kara jaddada cewar ba zasu bari Saraki ya cigaba da mulkar su a matsayin shugaban majalisar dattawa ba, tunda har ya canja sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Zamu tsige Saraki ko ta wane hali - Omo Agege

Zamu tsige Saraki ko ta wane hali - Omo Agege

A cikin satin nan ne Sanatocin jam'iyyar APC suka gana da shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, domin neman mafita akan Saraki.

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

Sanatan yace, "Muna da labarin cewa suna kokarin su hade majalisun biyu, mu kuma baza mu taba yarda hakan ya faru ba. Saboda yanzu haka Saraki ya san cewa mun cika adadin da zamu iya cire shi daga kujerar shi. Saboda haka da mun samu wata dama zamu yi amfani da ita domin tsige shi daga kujerar ta shi."

A martanin da Saraki ya mayar ta bakin mai bashi shawara a fannin yada labarai, Yusuph Olaniyonu, ya yi Allah wadai da zargin da Sanatan yake yi, inda ya bayyana cewa wadanda suke so su tsige shi din sune babbar matsalar kasar nan ba shi ba.

Ya ce, "Muna kokari muga mun rike mukaman mu, saboda da yawa a cikin masu son tsige ni maciya amana ne, don haka baza mu bari hakan ya faru ba. Da akwai da yawa a cikin su wanda ya kamata ace yanzu haka suna gidan kurkuku, saboda irin abubuwan da suka aikata. Amma saboda kariya da suke samu daga wurin gwamnati shine yasa har suke da bakin magana."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel