2019: El-Rufa'i ya gargadi jam'iyyar APC

2019: El-Rufa'i ya gargadi jam'iyyar APC

A yayin da zabukan shekarar 2019 ke kara matsowa, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya gargadi masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC da kada su goyi bayan duk wani dan takara da bashi da nagarta.

Elrufa'i na wannan kalamai ne a jiya Juma'a yayin halartar taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a garin Maigana, shelkwatar karamar Soba.

Gwamnan ya bayyana cewar bashi da niyyar goyon bayan kowanne dan takarar tare da bukatar jama'a su yi karatun ta natsu a kan duk neman takara kafin su zabe su.

2019: El-Rufa'i ya gargadi jam'iyyar APC

Malam Nasir El-Rufa'i

"Jama'a ya kamata su san 'yan takara nagari domin damar zaben shugabanni masu nagarta na hannun ku.

"Ba zamu tsoma baki ko kokarin yin cushen 'yan takara ba, ku ne zaku zabi duk wanda ku ke ganin yafi dacewa", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN) ya rawaito El-Rufa'i na fada.

DUBA WANNAN: An yankewa magidanci mai 'ya'ya 7 hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kazalika ya yi kira ga duk wadanda suka kai munzalin yin da su mallaki katin zabe na dun-dun-dun domin zabar shugabannin da suke so.

Sannan ya kara da basu shawarar cewar su yi amfani da damar karin wa'adin rijistar zabe da hukumar INEC tayi domin mallakar katin zaben.

"Ina so na jaddada maku muhimmancin mallakar katin zabe domin katin ku shine kuri'ar ku kuma kuri'ar ku ita ce makamin ku," in ji El-Rufa'i.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel