Mahaifar Shugaba Buhari ta shirya tsaf domin isowar sa

Mahaifar Shugaba Buhari ta shirya tsaf domin isowar sa

A ranar yau ta Asabar ne ake ake ci gaba da kiradadon dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga hutun kwanaki goma da ya tafi Birnin Landan na kasar Birtaniya a makonnin da suka gabata.

Shugaban kasar ya fice daga Najeriya bayan sanar da hakan ga majalisar dokoki ta tarayya cikin wata rubutacciyar wasika makonni biyu da suka gabata. A yayin tafiyar sa ya kuma danka ragamar mulkin kasar nan a hannun mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Mallam Garba Shehu, Mai magana da yawun shugaban kasar shine ya bayar da tabbacin dawowar Ubangidansa a yau cikin wata sanarwa da ya bayyana a ranar Juma'ar da ta gabata.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, shugaban kasar zai kuma kama hanyar mahaifarsa ta Garin Daura dake jihar Katsina a gobe Lahadi ko kuma Litinin domin gudanar da bikin babbar Sallah kamar yadda saba a koda wane lokaci.

Mahaifar Shugaba Buhari ta shirya tsaf domin isowar sa

Mahaifar Shugaba Buhari ta shirya tsaf domin isowar sa

Rahotanni sun bayyana cewa, hadiman shugaban kasar tuni sun isa garin na Daura domin fara gudanar da shirye-shiryen na isowar Uban gidan su.

KARANTA KUMA: Bikin Sallah: Gwamna Ganduje zai biya Ma'aikata Albashin watan Agusta a jihar Kano

Bisa al'ada shugaba Buhari ya saba gudanar da bukukuwan Sallah a kowace shekara tare da 'yan uwan sa a mahaifar ta sa dake jihar Katsina.

Kazalika dangane da tanadin sashe na 145 cikin kundin tsari, shugaba Buhari na da cikakkiyar dama ta daukar hutun aiki inda kuma zai mika ragamar mulkin kasar sa a hannun mataimakin sa kamar yadda ya aiwatar cikin wata rubutacciyar wasika a ranar 1 ga watan Agusta da hadiman sa, Mista Femi Adesina ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a zaurukan sada zumunta kamar haka:

https://www.business.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel