Saraki ya ziyarci Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel

Saraki ya ziyarci Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya kai wata muhimmiyar ziyarar ga gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel tare da yaba ma sa kan tsayuwar daka bisa jagorancin jihar.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, wannan ziyara wani yunkuri na kausasawa tsohon shugaban majalisar dattawa maras rinjaye, Sanata Godswill Akpabio, wanda a halin yanzu ya zamto abokin adawa da hamayya ga Saraki.

A ranar 8 ga watan Agustan da ta gabata ne aka gudanar da bikin sauye shekar Ubagngida ga gwamna Emmanuel kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Akpabio daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC a farfajiyar wasanni dake garin Ikot Ekpene.

Wannan farfajiya ta tumbatsa da al'umma yayin da kuma Sanatan ya yi murabus daga kujerar sa ta PDP na shugaban Majalisar dattawa maras rinjaye.

Saraki ya ziyarci Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel

Saraki ya ziyarci Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel

Saraki wanda a halin yanzu ya zamto wani jigo na jam'iyyar PDP da ya sauya sheka daga jam'iyya mai ci ta APC a kwana-kwanan nan ya bayyana cewa, ya ziyarci jihar ne domin nuna goyon baya da kuma aiwatar da kara ga gwamna Emmanuel.

Saraki ya bayar da tabbacin sa ga gwamnan da cewar wakilan jam'iyyar PDP dake majalisar dokoki ta tarayya za su ci gaba da bayar da hadin kai gami da goyon baya a gare sa domin ci gaba da kwararawa al'ummar jihar sa romo na dimokuradiyya.

KARANTA KUMA: Matsaloli 3 da Jam'iyyar PDP za ta fuskanta yayin Zaben fitar da 'Dan Takara

A nasa jawaban, Gwamna Emmanuel ya nemi shugaban Majalisar dattawa akan ci gaba da sauke nauyin al'ummar kasar nan da ya rataya a wuyan sa kamar yadda ya saba.

Legit.ng ta fahicmi cewa, tawagar Saraki da ta ziyarci fadar gwamna Emmanuel ta hadar da; Sanata Dino Melaye, Clifford Odia na jihar Edo da kuma Sanata Bassey Akpan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel