Gida yayi kira: Shugaba Buhari ya kammala hutun sa, yau zai dawo gida

Gida yayi kira: Shugaba Buhari ya kammala hutun sa, yau zai dawo gida

A yau Asabar ne dai ake kyautata zaton shugaba Muhammadu Buhari zai dawo gida Najeriya bayan shafe kimanin sati biyu yana hutawa a birnin Landan dake a kasar Ingila.

Fadar shugaban kasar dai ta bayyana cewa tuni shugaban ya kammala dukkan shire-shiren sa na dawowa sannan suma sun shirya tsaf domin tarbar ta sa.

Gida yayi kira: Shugaba Buhari ya kammala hutun sa, yau zai dawo gida

Gida yayi kira: Shugaba Buhari ya kammala hutun sa, yau zai dawo gida

KU KARANTA: Yan sanda sun cafke masu kera bindigogi a Kano

Legit.ng dai ta samu cewa wasu jama'ar kasar tuni suka fara korafin cewa shugaban kasar ya wuce adadin kwanakin da ya dauka, zargin da fadar shugaban kasar ta karyata.

Bayan tafiyar sa dai, mataimakin sa ne Farfesa Yemi Osinbajo ya rike kasar kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel