An samu nasarar ceto mutane bakwai daga benen da ya rushe a Abuja

An samu nasarar ceto mutane bakwai daga benen da ya rushe a Abuja

Hukumomin agajin gaggawa dake babban birnin tarayya wato NEMA, sun cinye daren jiya a tsaye suna kokarin ceto mutanen da ake tunanin suna karkashin benen da ya rufta da su

An samu nasarar ceto mutane bakwai daga benen da ya rushe a Abuja

An samu nasarar ceto mutane bakwai daga benen da ya rushe a Abuja

Hukumomin agajin gaggawa dake babban birnin tarayya wato NEMA, sun cinye daren jiya a tsaye suna kokarin ceto mutanen da ake tunanin suna karkashin benen da ya rufta da su.

Sai dai kuma har ya zuwa wannan lokacin alamu na nuna cewa babu wanda wasu mutane da suka yi saura a cikin ginin, kamar dai yanda wani jami'in hukumar bada agajin gaggawar yayi bayani, ya shaidawa maneman labarai cewa, kawo yanzu mutum bakwai ne suka samu rauni, sannan mutum daya ya rigamu gidan gaskiya.

DUBA WANNAN: Babbar jam'iyyar adawa PDP ta bawa wani tsohon minista babban mukami

Ginin dai ya rufta ne a jiya Juma'a, a unguwar Jabi dake babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

A yanzu haka dai ana ta faman kokarin dauke karafen da aka yi amfani dasu wurin yin ginin domin samun damar kashe baraguzan bene, wanda ake tunanin sun danne mutane.

Wata majiyar na nuna cewa cikin wadanda lamarin ya rutsa dasu har mata. Har ya zuwa yanzu dai ba a san ainahin adadin mutanen dake cikin ginin ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel