An kai mummunan hari masallatan juma'a guda 2 a lokaci daya

An kai mummunan hari masallatan juma'a guda 2 a lokaci daya

An kai wasu hare - hare guda biyu a jere a wasu manyan masallatan juma'a dake garin Bermingham a kasar Ingila

An kai mummunan hari masallatan juma'a guda 2 a lokaci daya

An kai mummunan hari masallatan juma'a guda 2 a lokaci daya

An kai wasu hare - hare guda biyu a jere a wasu manyan masallatan juma'a dake garin Bermingham a kasar Ingila. Sanarwar da kafafen yada labarai suka fitar, sun bayyana cewa an kai harin a masallatan da suke a yankunan da musulmai suke da yawa.

DUBA WANNAN: Babbar jam'iyyar adawa PDP ta bawa wani tsohon minista babban mukami

Sanarwar ta bayyana cewa an kai harin na farko da misalin karfe 10 na dare a lokacin da ake gabatar da sallar Isha'i a masallacin Kamarul Islam, sannan kuma an kai hari na biyu bayan mintuna 20 a tsakani a masallacin Al-Hijra.

Hukumar 'yan sandan garin na Bermingam sun bayyana cewa, an farfasa gilasan masallatan a yayin da aka kai harin, sannan kuma an kai jami'an kashe gobara masu yawa yankin da abin ya shafa.

Hukumomin sun fara gabatar da bincike akan harin da babu wanda yaji ciwo.

Al'ummar musulman kasar ta Ingila sun yi Allah wadai da harin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel