Neman gindin zama: Saraki ya ziyarci wani gwamna

Neman gindin zama: Saraki ya ziyarci wani gwamna

A ranar juma'ar nan ne shugaban majalisar dattawa na Najeriya, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya ziyarci gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel

Neman gindin zama: Saraki ya ziyarci wani gwamna

Neman gindin zama: Saraki ya ziyarci wani gwamna

A ranar juma'ar nan ne shugaban majalisar dattawa na Najeriya, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya ziyarci gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, inda ya jinjina masa da irin namijin kokarin da yake yi a jihar.

Mai gidan Emmanuel, sannan kuma tsohon gwamnan jihar ta Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio, ya canja sheka a ranar 8 ga wannan watan daga babbar jam'iyyar adawa PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC. Bikin murnar komawar tashi wanda aka gabatar a babban filin wasa na Ikot Ekpene ya janyo hankalin mutane masu dumbin yawa, tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar ta APC. Bayan haka kuma Akpabio ya ajiye mukamin sa na shugaban marasa rinjaye na jam'iyyar PDP a majalisar dattawa.

DUBA WANNAN: Babbar jam'iyyar adawa PDP ta bawa wani tsohon minista babban mukami

Saraki wanda a yanzu yake daya daga cikin jigo a jam'iyyar PDP, shi ma bai jima da canja sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP ba. Ya ce ya kai ziyarar ne domin ya nuna goyon bayan shi ga gwamnan jihar.

Ya yiwa gwamnan alkawarin cewa jam'iyyar PDP zata cigaba da kokari wurin bashi goyon baya da kwarin guiwa domin cigaba da ayyuka na alkairi ga al'umma.

Ya bukaci gwamnan da ya cigaba da kokari wurin gabatar da ayyukan cigaba ga al'ummar jihar, inda ya ce ya tabbata mutanen jihar suna tare dashi dari bisa dari. Sannan ya kara da cewa Emmanuel kada yaji tsoron komai tunda yana da goyon bayan majalisar tarayya, majalisar jiha, shugabannin kananan hukumomi da sauran su, kowa yana goyon bayan shi.

A lokacin da yake bayanin shi, gwamnan ya bukaci Saraki da ya cigaba da ayyukan alkhairin da yake na kawo cigaba da kare Najeriya daga mugan mutane. A karshe gwamnan yayi amfani da damar shi wurin yiwa Saraki maraba da dawowa jam'iyyar PDP, inda ya kara da cewa mutanen jihar Akwa Ibom suna tare dashi dari bisa dari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel