Shugaba Buhari ya kira Gwamna Dickson domin yi masa ta’aziyya

Shugaba Buhari ya kira Gwamna Dickson domin yi masa ta’aziyya

Mun ji labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kira Gwamnan Jihar Bayelsa Seriake Dickson domin yi masa ta’aziyyar rashin Mahaifiyar sa da yayi kwanakin baya a Kasar waje.

Shugaba Buhari ya kira Gwamna Dickson domin yi masa ta’aziyya

Buhari ya kira Gwamnan Bayelsa Dickson bayan Uwar sa ta rasu
Source: Depositphotos

Shugaba Buhari ya nemi Gwamnan na Bayelsa a wayar salula domin yi masa gaisuwar rashin Mahaifiyar sa Madam GoldCoast Dickson mai shekaru 72 da ta cika kwanaki a wani babban asibiti da ake ji da shi a Amurka.

KU KARANTA: Yunwa ta kashe mutane 33 a Jihar Borno a lokacin Buhari

Shugaban kasar na Najeriya wanda yanzu ba ya nan ya kira Gwamnan ne jiya kamar yadda mu ka samu labari daga Fadar Shugaban kasa. Hadiman Shugaban kasar ne su ka bayyana wannan a shafin sa na sada zumunta na Tuwita.

A halin yanzu dai Shugaba Buhari yana Landan inda ya tafi hutun kwana 10. Manyan kasar nan da dama sun yi wa Gwamna Seriake Dickson ta’aziyya bayan cutar kansar mama ta kashe Mahaifiyar sa a Garin Texas a cikin watan nan.

Idan ba ku manta ba Babban Sakataren Gwamnatin Jihar Bayelsa Francis Ottah-Agbo ya sanar da rasuwar Mahaifiyar Gwamnan. Madam Dickson ta rasu ne a wani asibitin da ke kula da kansa a a Garin Houston a Jihar Texas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel