Boko Haram: Gwamnatin Tarayya ta karyata zargin UN game da Matan Dapchi

Boko Haram: Gwamnatin Tarayya ta karyata zargin UN game da Matan Dapchi

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bakin Ministan yada labarai ta karyata zargin Majalisar Dinkin Duniya na cewa an biya ‘Yan Boko Haram kudi kwanaki domin sakin wasu mata da aka sace.

Boko Haram: Gwamnatin Tarayya ta karyata zargin UN game da Matan Dapchi

Ana zargin Najeriya ta biya 'Yan Boko Haram kudi kan Matan Dapchi

Jiya kun ji cewa wani kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ‘Yan ta’addan Boko Haram sun samu kudi daga hannun Gwamnatin Najeriya bayan sun sace wasu ‘Yan makaranta sun yi garkuwa da su kwanaki.

Wannan batu ya jawo ana ta cacar baki tsakanin Gwamnatin kasar da Majalisar Dinkin Duniya inda Ministan yada labarai Lai Mohammed yace zargin da UN ta ke yi bai da wani tushe domin Gwamnatin Kasar ba ta biya sisin kobo ba.

KU KARANTA: Wani gini ya rushe da mutane a Garin Abuja

Lai Mohammed yace Majalisar ta UN ba ta da wata hujja ta kusa ko ta nesa da za tace Najeriya ta biya ‘Yan ta’addan Boko Haram kudi domin su saki ‘Yan matan Makarantar Dapchi na Jihar Yobe da aka sace a cikin farkon shekarar nan.

Ministan yace abin da dai ya faru shi ne a lokacin an shiga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Jami’an tsaron Najeriya da ‘Yan Boko Haram, don haka ne dole ‘Yan ta’addan su ka dawo da matan da su ka sace ba tare da an biya taro ba.

Kun ji labari cewa an gano yadda ‘Yan Boko Haram ke samun kudin shiga a Najeriya. ‘Yan kungiyar Boko Haram na samun kudi daga Kungiyoyi na NGO da kuma satar ‘Yan mata da sauran mutane su yi garkuwa da su har sai an bada kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel