INEC ta saki sanarwan zaben 2019 a Lagas

INEC ta saki sanarwan zaben 2019 a Lagas

Duk a cikin shirye-shiryen zaben 2019, hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Lagas a ranar Juma’a, 17 ga watan Agusta ta wallafa sanarwar zabe a ofishinta na jihar, ofishohinta na kananan hukumomi da kuma yankunan da take rijista a jihar.

INEC ta bayar da wannan umurni ne a wata sanarwa daga kakakinta, Mista Femi Akinbiyi.

“Matakin yayi dadai ne da ranar da aka amince na gudanar d zabukan 2019, kamar yadda yake a sashi 30 a dokar zabe,” inji Akinbiyi.

Dokar zaben ya bayyana cewa: “Hukumar ba zata wallafa wata sanarwa akalla kwanaki 90 ranar da aka sanya domin gudanar da zabe a kowani jiha na tarayyar kasar da babban birnin taraya”.

INEC ta saki sanarwan zaben 2019 a Lagas

INEC ta saki sanarwan zaben 2019 a Lagas

Akinbiyi yayi bayanin cewa dokar ta bukaci hukumar ta bayyana ranar zabe da kuma wajen da za’a rarraba takardun.

KU KARANTA KUMA: Fashin Offa: Kotu tayi barazanar tura IGP gidan yari kan zargin saba mata Fashin Offa: Kotu tayi barazanar tura IGP gidan yari kan zargin saba mata

Ya kara da cewa dokar ta kuma bukaci cewa a wallafa sanarwar a kowani mazaba da za’a gudanar da zabe.

Kamfanin dillancin laarai ta rahoto cewa za’a gudanar da zaen shugaban kasa da na majalisar dokoki a ranar 16 g watan Farairun 2019, yayinda gwamnoni da nay an majalisun jiha zai zo a ranar 2 ga watan Maris.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel