Ni ya dace in canji Obasanjo tun a 2007 don haka ni ya kamata a ba tikitin 2019 – Makarfi

Ni ya dace in canji Obasanjo tun a 2007 don haka ni ya kamata a ba tikitin 2019 – Makarfi

Da alamu dai sai an yi da gaske wajen fitar da ‘Dan takarar Shugban kasa a Jam’iyyar adawa ta PDP bayan an ji tsohon Gwamnan Kaduna Sanata Ahmad Makarfi yana wasu maganganu daf da zaben.

Ni ya dace in canji Obasanjo tun a 2007 don haka ni ya kamata a ba tikitin 2019 – Makarfi

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Makarfi yana neman PDP ta tsaida sa
Source: Depositphotos

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP kuma tsohon Gwamna Jihar Kaduna daga 1999 zuwa 2007 Ahmad Muhammad Makarfi ya bayyana cewa da karfi da yaji aka hana sa tikitin takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP a 2007.

KU KARANTA: Lokacin tsayawa takarar Saraki yayi - Inji Kawu Baraje

Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ya ziyarci Kudancin Najeriya domin cigaba da yakin neman zaben fitar da gwani na PDP. Makarfi ya nemi ‘Yan PDP su tuna da wahalar da yayi da Jam’iyyar lokacin ana fama da adawa a kasar.

Tsohon Gwamnan wanda ya nemi goyon-bayan manyan Jam’iyyar PDP a Jihar Delta inda ya tuna masu cewa shi ya kamata yayi mulki a 2007 amma aka yi kutun-kutun aka hana sa takara a PDP. A lokacin Marigayi ‘Yaradua yayi nasara.

Ahmad Makarfi wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa tsakanin 2007 zuwa 2015 kuma ya rike Jam’iyyar PDP a lokacin da ake cikin rikici a Jam’iyyar. Makarfi yana cikin manyan masu takarar Shugaban kasa a PDP

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel