Yunwa ta kashe yara 33 a Borno – kungiyar MSF

Yunwa ta kashe yara 33 a Borno – kungiyar MSF

Kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta sanar da cewa ta kaddamar da taimakon gaggawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya bayan mutuwar akalla yara 33 a sansanin 'yan gudun hijira da ke Borno.

MSF ta ce yaran sun mutu ne tsakanin ranakun 2 zuwa 15 ga watan Agusta a sansanin 'yan gudun hijirar da ke Bama a Jihar Borno.

An kiyasta cewa akwai yara kusan dubu shida 'yan kasa da shekara 5 a sansanin da ke fuskantar wannan barazanar.

MSF ta ce a yanzu ta soma ba da tallafin gaggawa na abinci mai gina jiki, da magunguna tsakanin yaran da ke sansanin.

Yunwa ta kashe yara 33 a Borno – kungiyar MSF

Yunwa ta kashe yara 33 a Borno – kungiyar MSF

Ana dangata yanayin damina da karuwar matsalolin lafiya irinsu zazzabin cizon sauro da sauran cututtuka masu yaduwa a sansanin.

KU KARANTA KUMA: Ba ni da niyar komawa PDP – Inji na hannun daman Atiku

Sai dai Hukumar dake bayar da agajin gaggawa wato NEMA ta ce tana da masaniya akan karuwar tamowa a sansanin Bama, amma ta musanta adadin yaran da kungiyar ke cewa sun mutu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel