An sace direbobin mota 51 a jihar Kebbi - Bagudu

An sace direbobin mota 51 a jihar Kebbi - Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya ce an sace direbobi sama da 51 yayin da su kayi zagaye a hanyarsu ta zuwa Birnin Kebbi saboda rashin kyawun hanyar data hade da Yauri.

A jawabin da gwamnan ya yi jiya a wajen taron Cbiyar Ayyuka na kasa, ya ce yana matukar damuwa da irin wahalhalun da direbobin ke fuskanta a kowacce rana saboda rashin kyawun tituna.

An sace direbobin mota 51 a jihar Kebbi - Bagudu

An sace direbobin mota 51 a jihar Kebbi - Bagudu

Ya ce: "Direbobin sun fada min dole yasa suke zagaye a Bargu dake jihar Neja dake karamar hukumar Magama idan suna hanyar tafiya ko dawowa Kebbi daga Legas. Wahalhalun da suke fuskanta daga 'yan fashi da masu garkuwa da mutane ya tsananta."

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya gaji sama da ayyukan tituna 200 da ba'a kammala ba ko aka watsar wanda kudinsu ya kai N2 tiriliyan amma N500 biliyan kawai gwamnatin da ta shude ta biya.

Ministan ya ce babu wata jiha da gwamnatin tarayya bata gudanar da wata muhimmiyar aikin gine-gine.

Ya ce wasu 'yan kwangilan, Injiniyoyi da Leburori sunyi watsi da ayyukan saboda matsalar rashin tsaro kuma gwamnati kuma akwai kudade masu yawa da gwamnati ya kamata ta biya su.

Fashola ya yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya, da malaman addini da shugabanin al'umma su bawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari goyon bayan a yunkurinta na dawo da zaman lafiya a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel