Fashin Offa: Kotu tayi barazanar tura IGP gidan yari kan zargin saba mata

Fashin Offa: Kotu tayi barazanar tura IGP gidan yari kan zargin saba mata

Wata babbar kotu dake Ilorin, babban birnin jihar Kwara tayi barazanar tura sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris gidan kurkuku kan zargin saba umurnin kotu.

Kotun karkashin jagorancin Justis Ibrahim Yusuf ta yanke wannan hukunci a daidai da tsarin kin biyayya ga umurnin kotu (fam 48).

Umurnin mai kwanan wata 10 ga watan Agusta, 2018 na dauke da sa hannun magatakardan kotun sannan kuma an mika ga IGP, hedkwatar rundunar dake Abuja.

Fashin Offa: Kotu tayi barazanar tura IGP gidan yari kan zargin saba mata

Fashin Offa: Kotu tayi barazanar tura IGP gidan yari kan zargin saba mata

Umurninya biyo bayan kin bin umurnin baya da akayi na sakin hadimin gwamna Abdulfatah Ahmed, Olalekan Alabi.

Yan sanda sun kama Alabi a ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, kan zargin nasabarsa da wadanda suka yi fashin Offa.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai dawo Abuja a ranar Asabar

Kotu ta ba Alabi beli, inda yan sanda kuma suka ki sakinsa kusan watanni biyu.

Don haka duk da umurnin kotu Alabi na nan a tsare inda yan sanda suka ki sakinsa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel