Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a saki ma'aikatan agaji 3 da Boko Haram suka sace

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a saki ma'aikatan agaji 3 da Boko Haram suka sace

A yau Juma'a ne Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a saki ma'aikatan agaji guda uku da Boko Haram ta sace yayin da suke aikin agaji a garin Rann dake karamar hukumar Kalabalge ta jihar Borno.

Mai kula da ayyukan hukumar na Najeriya, Mr Edward Kallon ne ya yi wannan kira yayin da ya ziyarci Gwamna Kashim Shettima a fadar gwamnati da ke Maiduguri.

Kamfanin dillanci labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa 'yan Boko Haram sun kai hari a kauyen Rann a watan Mayun wannan shekarar a wata sansanin 'yan gudun hijira mai nisar kilomita 150km yammacin Maiduguri.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a saki ma'aikatan agaji 3 da Boko Haram suka sace

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a saki ma'aikatan agaji 3 da Boko Haram suka sace

An ruwaito cewa mayakan kungiyar ta'addancin sun kashe wasu masu gadin kafin su kayi awon gaba da ma'aikatan bayar da agajin.

DUBA WANNAN: Har yanzu bamu wanke Saraki daga maganar Offa ba - Malami

A jawabin da ya yi a don murnar zagoyowar ranar Agaji ta Duniya, Kallon ya yi Allah wadai ta sace ma'aikatan da akayi yayin da suke bayar da taimakon da magunguna ga 'yan gudun hijira da ke sansanin.

"Kashe jami'in hukumar NEMA da akayi a Damasak makon da ta gabata alama ce da ke tunatar damu irin hadarurukan da ke tattare da aikin bayar da agaji," inji wakilin Majalisar Dinkin Duniya.

Kallon ya yi kira da bangarorin da ke fada da juna su bari masu aikin bayar da agaji suyi ayyukansu na taimakon mutanen da ke cikin fitina kamar yadda dokar kasa da kasa na agaji ta tanada.

Ya kuma kira ga gwamnatin Najeriya ta bawa ma'aikatan agaji dake taimakon jama'a a wuraren da ake fama da tashe-tashen hankula kariya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel