Ba ni da niyar komawa PDP – Inji na hannun daman Atiku

Ba ni da niyar komawa PDP – Inji na hannun daman Atiku

Wani tsohon mukaddashin gwamnan jihar Adamawa kuma na hannun daman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a harkar siyasa, Ambasada James Barka ya karyata sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress zuwa Peoples Democratic Party.

Ya bayyana cewa gaskiya ne cewar jam’iyyar PDP reshen jihar sun kawo masa ziyarar ban girma a gidansa dake Yola wanda anan ne suka ja hankalinsa da ya koma ja’iyyar, ya kara da cewa bai yi alkawarin komawa jam’iyyar ba.

Ba ni da niyar komawa PDP – Inji na hannun daman Atiku

Ba ni da niyar komawa PDP – Inji na hannun daman Atiku

Barka, a wata sanarwa da ya saki a Abuja a ranar Juma’a, 17 ga watan Agusta yace bashi da niyar komawa PDP wacce ya bari a 2014 yayinda yake jakadan Najeriya a kasar Malaysia.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi kira ga majalisar dokokin kasar da su dawo zama a tare da bata lokaci ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai dawo Abuja a ranar Asabar

Jam’iyyar tayi wannan kira ne a ranar Juma’a a wata sanarwa daga mukaddashin sakataren labaranta, Mista Yekini Nabena.

Ta bukaci bangaren dokoki da suyi gaggawar kula da muhimmancin kasafin kudin hukumar zabe mai zaman kanta domin zaben shekara mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel