Buhari zai dawo Abuja a ranar Asabar

Buhari zai dawo Abuja a ranar Asabar

Ana sanya ran dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari kasar a ranar Asabar, 18 ga watan Agusta bayan hutun kwanaki 10 da ya tafi a birnin Landan.

Manyan jami’an gwamnati kakashin jagorancin mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zasu tarbi shugaban kasa Buhari a yayinda zai sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport dake babban birnin tarayya Abuja.

Buhari zai dawo Abuja a ranar Asabar

Buhari zai dawo Abuja a ranar Asabar

An tattaro cewa shugaban kasar ya shirya zuwa Daura a karshe makon nan domin ya samu damar yin bikin babban Sallah wato Eid-el-kabir a mahaifarsa.

A halin da ake ciki, Mai martaba sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar zai nadawa Dr Orji Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia sarautar Dan Baiwan Daura.

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole majalisa ta dawo zama ba tare da bata lokaci ba – APC

Sarkin a wata wasika mai kwanar wata 9 ga watan Agusta yace masarautar Daura ta yanke wannan shawara domin karrama Kalu, wadda ya kasance jigon jam’iyyar Progressive Congress (APC).

A cewar wata sanarwa daga Mista Kunle Oyewumi, kakakin Kalu, za’ayi bikin ne a lokacin babban Sallah.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel