Da duminsa: Wani katafaren gini ya rushe a Abuja, ya danne ma'aikata

Da duminsa: Wani katafaren gini ya rushe a Abuja, ya danne ma'aikata

Mutum daya ya rasu yayin da wasu goma sun makale a kasan gini yayin da wata bene mai hawa uku a ake ginawa a unguwar Jabi da ke babban birnin tarayya Abuja ta rushe a yau Juma'a.

Lamarin ya afku ne misalin karfe 1.20 zuwa 2.00 na rana yayin da ma'aikata ke aiki.

An gano cewa cikin wanda ginin ya danne su harda magina da yara kanana da masu sayar da abinci.

An gano cewa an ceto mutane takwas yayin da mutum daya ya riga mu gidan gaskiya. Cikin wadanda aka ceto har da wani Injiniyan gini wanda kafafuwansa biyu suka karye.

Da duminsa: Wani katafaren gini ya rushe a Abuja, ya dane ma'aikata

Da duminsa: Wani katafaren gini ya rushe a Abuja, ya dane ma'aikata

DUBA WANNAN: An kai karar sanata kotu kan sauyin sheka, kotu ta aiko sammaci

A lokacin rubuta wannan rahoton, jami'an hukumar agajin gagawa na kasa NEMA da jami'an hukumar kiyaye gobara na sun hallara kuma suna kokarin taimakawa mutanen da abin ya rutsa dasu.

An gano cewa an fara ginin ne tun shekaru 15 fda suka gabata amma cikin kwanakin nan 'yan kwangilan da ke aikin suka tattaro ma'aikata domin cigaba da aikin.

Ku cigaba da biyo mu domin samun karin bayani...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel