Matashiya 'Yar Shekaru 36 ta sanya Budurcinta kan $283,466 a Kasuwa

Matashiya 'Yar Shekaru 36 ta sanya Budurcinta kan $283,466 a Kasuwa

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wata Matashiyar kasar Jamus 'yar shekaru 36 kuma mai rike da mutuncin ta, ta sanya budurcinta a kasuwa kan Dalar Amurka 283,466, kimanin Naira miliyan dari kenan a kudin Najeriya.

Matashiyar mai sunan Mandy wadda ma'akaciyar wani kamfanin jiragen sama ce ta tallata budurcin na ta da taimakon shafin Kamfanin Cindrella Escorts na yanar Gizo.

Mandy ta samu masaniyar wannan kamfani ne cikin shafin wata jarida inda ta cimma nasara yayin da wani hamshakin dan kasuwa na birnin Munich da aka sakaya sunan sa ya saye nan take kamar yadda jaridar Daily Mail ta bayyana.

Matashiya 'Yar Shekaru 36 ta sanya Budurcinta kan $283,466 a Kasuwa

Matashiya 'Yar Shekaru 36 ta sanya Budurcinta kan $283,466 a Kasuwa

Matashiyar mai sha'awar sana'ar wake-wake ta shafe tsawon rayuwarta ne ba tare da kusantar wani da namiji ba sakamakon ci gaba da tsimayen Mutumin da ya dace tayi tarayya da shi.

KARANTA KUMA: Ba zan iya aiki ba tare da zuƙar Tabar Wiwi ba - Wani Mutum ya shaidawa Kotu

Ta kuma bayyana cewa, ta sanya budurcin ta ne a kasuwa domin samun hanyar da za ta cimma burin ta na kasancewa mashahuriyar mawakiya a duniya, yayin da 'yan kudade suka zauna ma ta a hannu.

Rahotanni sun bayyana cewa, kasuwar budurcin Mandy ta kasance tamkar wani gidan caca inda aka samu wani lauya da ya sanya dalar Amurka 273768 yayin da wani dan wasan kwallon kafa ya sanya dalar Amurka 228140 domin biyan bukatun su na lokaci guda kacal.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a zaurukan sada zumunta kamar haka:

https://www.business.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel