Dalilin da yasa gwamnoni basu iya samarwa jama'a ababen more rayuwa - Gwamna Yari

Dalilin da yasa gwamnoni basu iya samarwa jama'a ababen more rayuwa - Gwamna Yari

Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce rashin kudade ne yake hana gwamnoni samarwa jama'a ababen more rayuwa a fanonin kiwon lafiya, ilimi, ginin tituna da sauransu.

Ya ce hakan ne yasa gwamnonin kawai suka kasance basu iya aikata komai sai dai biyan albashi a jihohinsu. Ya kara da cewa babu wata siddabaru da zasu gwamnonin zasu iya saboda babu kadaden da zasu gudanar da ayyukan.

Kamar yadda Punch ta ruwaito, Mr Yari ya yi wannan furucin ne bayan an kammala taron gwamoni da aka yi a Abuja a ranar Laraba.

Abinda ke hana gwamnoni samarwa jama'a ababen more rayuwa - Gwamna Yari

Abinda ke hana gwamnoni samarwa jama'a ababen more rayuwa - Gwamna Yari

Mr Yari, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya yi kira da mahukunta su sake duba albashin ma'aikata na shekaru 14 da suka gabata saboda su san yadda za'a tsayar da sabuwar mafi karancin albashi.

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

Kwamitin da ke aiki kan mafi karancin albashin sun gama tattaunawarsu. Gwamnatin tarayya ta ce za'a fara biyan mafi karancin albashin ma'aikatan daga watan Satumban wannan shekarar.

Gwamnonin na juyayiin irin abubuwa da ka iya biyo baya bayan an amince da mafi karancin albashin yayin da Kungiyar Kwadaga na kasa NLC ta dage akan cewa ya kamata mafi karancin albashin ya fara daga N65,000.

"Muna da kwamitin mutane shida da ke wakiltan mu a tattaunawar da ake yi game da mafi karancin albashin da Ministan Kwadago ke jagoranta," inji shi.

Gwamna Yari kuma ya ce gwamnonin sun tattauna kan yadda hukumomin yaki da rashawa ke gudanar da yaki da rashawar inda suka amince da cewa ya zama dole hukumomin suyi aikinsu kan ka'ida doka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel