Ku bi ta kan Buhari tunda ya ki sanya hannu a dokar zabe – PDP ga majalisar dokoki

Ku bi ta kan Buhari tunda ya ki sanya hannu a dokar zabe – PDP ga majalisar dokoki

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci majalisar dokoki da ta bi ta kan shugaban kasa Muhamadu Buhari kan kin amincewa da yin gyara a dokar zabe.

Babban sakataren labarai na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan a wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta yayi zargin cewa shugaban kasar rike dokar zabe da shugaban kasar yayi daidai ne da garkuwa da kasar Najeriya domin kudin fansa.

“Jam’iyyar PDP na kira ga majalisar dokokin kasar da ta bi ta kan shugaba Buhari tunda kin sanya hannu da yayi a dokar gyara zabe son zuciya ne maimaikon bin ra’ayin kasa,” inji kakakin jam’iyyar.

Ku bi ta kan Buhari tunda ya ki sanya hannu a dokar zabe – PDP ga majalisar dokoki

Ku bi ta kan Buhari tunda ya ki sanya hannu a dokar zabe – PDP ga majalisar dokoki

A halin da ake ciki, shugaban kwamitin jihar Yobe na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Alhaji Adamu Chilariye, ya zargi jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da siyan katunan zaben wasu jama’a ba bisa doka ba.

KU KARANTA KUMA: Daruruwan mutane sun yi gangami a Jigawa domin marawa sanatan da ya koma PDP baya

Yayi zargin ne a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta a taron manema labarai a Damaturu. Legit.ng ta tattaro cewa ya bayyana cewa an sanarwa da kwamitin APC na jihar lamarin.

Don haka Chilariye ya shawarci jama’a da su yi taka tsan-tsan domin kada su fada a tarkon yan siyasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel