Takara 2019: Kwankwaso ya kai ma wani babban basaraken kasar Yarbawa ziyara

Takara 2019: Kwankwaso ya kai ma wani babban basaraken kasar Yarbawa ziyara

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ma babban basaraken jihar Oyo Alafin of Oyo ziyara a fadarsa dake jihar Oyo, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III ya karbi bakoncin Kwankwaso ne a kokarin Kwankwaso na neman goyon bayan tare da sa albarkar Basaraken a burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019.

KU KARANTA: Mugunta iya mugunta: Matasa 3 sun murɗe wuyan wani tsoho mai shekaru 105 har lahira

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya ga Oba Lamidi, Kwankwaso ya leka gidan tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Rashidi Adewolu Ladoja don neman goyon bayansa ga takararsa, sa’annan ya gana da shuwagabannin jam’iyyar PDP na jahar.

Takara 2019: Kwankwaso ya kai ma wani babban basaraken kasar Yarbawa ziyara

Kwankwaso da Alafin

Idan za’a tuna a yan kwanakin baya ne Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar APC, inda ya koma jam’iyyar PDP, inda ya hade tare da tsohon dan adawarsa da basa ga maciji, Malam Ibrahim Shekarau don su kada gwamnan Ganduje da shugaba Buhari a zaben 2019.

Duk da yake a baya basa jituwa, amma bukatar kai ta hada, kuma dukkaninsu sun bayyana cewa basu rike junansu a rai ba, don haka tafiya zata yi kyau.

Sai dai wasu bayanau sun nuna cewar shugabancin PDP ta kasa ta baiwa Kwankwaso iko da kasha 51 na jam’iyyar a Kano saboda ya shigo da yan majalisun tarayya guda shidda da kuma yan majalisun jaha guda tara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel