An tsinci jariri sabuwar haihuwa a kusa da wani gidan mai a garin Abuja

An tsinci jariri sabuwar haihuwa a kusa da wani gidan mai a garin Abuja

Hankulan al'ummar dake zaune a unguwar Kuje dake a garin Abuja, babban birnin tarayya sun tashi da safiyar yau biyo bayan tsintar wani jariri sabuwar haihuwa da akayi a kusa da wani gidan mai dake unguwar.

Jaririn dai kamar yadda muka samu, wasu matafiya ne suka lura da shi inda yake ajiye a nannade a cikin wani tsumma mai jike da jini a gefen gidan man Azman.

An tsinci jariri sabuwar haihuwa a kusa da wani gidan mai a garin Abuja

An tsinci jariri sabuwar haihuwa a kusa da wani gidan mai a garin Abuja

KU KARANTA: An kama wasu dalibai 2 suna badala a makarantar kwana

Legit.ng ta samu cewa tuni dai al'ummar unguwar suka sanar da 'yan sanda halin da ake ciki inda su kuma suka dauki jaririn suka kuma fara yin bincike game da lamarin.

A wani labarin kuma, Wani katon banza mai suna Promise Eshiet dake da shekaru akalla 53 a duniya ya shaidawa kotun majistare dake garin Ogba, can garin Legas yadda kyaun diyar sa ya labbace shi har yake kwana da ita.

Kamar dai yadda muka samu, diyar duka duka shekarun 13 a duniya amma ta shaidawa kotun cewa mahaifin nata na kwanciya da ita.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel