Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta rabe gida biyu a wata jiha a kudancin Najeriya

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta rabe gida biyu a wata jiha a kudancin Najeriya

Yanzu haka dai mun samu cewa harkokin siyasa na cigaba da daukar zafi a jihar Ribas dake a kudu maso kudancin kasar nan bayan da labarin bude wani sabon ofishin jam'iyyar adawa a jihar ta All Progressives Congress (APC) a zagaye gari.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu mafusatan matasan da ake kyautata zaton masu goyon bayan bangaren jam'iyyar da Sanata Magnus Ngei yake jagoranta sun farwa dayan bangaren.

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta rabe gida biyu a wata jiha a kudancin Najeriya

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta rabe gida biyu a wata jiha a kudancin Najeriya

KU KARANTA: Yadda wani malamin addini ya musuluntar da aljani a Saudiyya

Legit.ng ta samu cewa yanzu dai hakan na nufin jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC) ta rabe biyu kenan a jihar da bangaren tsohon gwamnan jihar Rotimi Amaechi da kuma bangaren Sanata Magnus.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman tikitin takarar shugaban kasa tare da shugaba Muhammadu Buhari, Alhaji Atiku Abubakar ya ce tattalin arzikin kasar nan bai taba tabarbarewa ba kamar a lokacin nan na mulkin shugaba Buhari.

Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabin sa ga dubban magoya bayan jam'iyyar sa ta PDP a garin Enugu jiya lokacin da ya kai ziyarar sada zumunci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel