Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun cafke masu kera bindigogi a jihar Kano

Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun cafke masu kera bindigogi a jihar Kano

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Kano sun sanar da samun nasarar cafke wasu mutane biyu watau Rabiu Suleman da kuma Yahaya Abdulkadir da suka kware wajen kera muggan bindigu da sauran miyagun makamai a karamar hukumar Tudun Wada.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar Musa Magaji Majia ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a jihar.

Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun cafke masu kera bindigogi a jihar Kano

Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun cafke masu kera bindigogi a jihar Kano

KU KARANTA: Wani dan Najeriya ya kwashi yan kallo a jami'ar Amurka

Legit.ng ta samu cewa sanarwa ta zayyana cewa sun muggan makaman da suka hada da bindigu 11 da kuma harsasai 53 a hannun hatsabiban takadaran.

Yanzu dai sun ce suna bincike kan lamarin kuma da zarar sun kammala za su maka su kotu.

A wani labarin kuma, Hankulan al'ummar dake zaune a unguwar Kuje dake a garin Abuja, babban birnin tarayya sun tashi da safiyar yau biyo bayan tsintar wani jariri sabuwar haihuwa da akayi a kusa da wani gidan mai dake unguwar.

Jaririn dai kamar yadda muka samu, wasu matafiya ne suka lura da shi inda yake ajiye a nannade a cikin wani tsumma mai jike da jini a gefen gidan man Azman.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel