Kudin zabe N189bn: Anyi baran-baran a ganawar yan majalisa da jami’an hukumar INEC

Kudin zabe N189bn: Anyi baran-baran a ganawar yan majalisa da jami’an hukumar INEC

Ba’a samu matsaya ba a ganawar sanatoci, mambobin majalisar wakilai da manyan jami’an hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC a ranan Alhamis, 16 ga watan Agusta, 2018.

Hukumar INEC ta bukaci majalisar dokokin tarayya ta bada daman a basu kudi N189bn domin gudanar da zaben 2019.

Anyi baran-baran a zaman da akayi a zauren majalisa saboda rashin daidaiton kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya bukata a baiwa INEC da kudin da shugaban INEC, Mahmoud Yakubu ya bukata.

KU KARANTA: Za’a ciyar da yan sanda da kudi N6bn kacal

Yayinda shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci N143bn, shugaban hukumar Mahmoud Yakubu ya bukaci N189bn.

Game da cewar shugaban kwamitin majalisar dattawan kan hukumar INEC, Sulaiman Nazif, kwamitin majalisun guda biyu zasu bayyanawa jama’a matsayarssu bayan ganawar da zasuyi a yau.

Yayinda yake jawabi ga manema labarai a Abuja bayan ganawar, Nazify a tabbatarwa yan Najeriya cewa yan majalisan za suyi iyakan kokarinsu wajen ganin hukumar INEC ta gudanar da zaben gaskiya cikin zaman lafiya da lumana a 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel