Jiragen dankaro guda 27 cike da kayan abinci makil sun tunkaro Najeriya

Jiragen dankaro guda 27 cike da kayan abinci makil sun tunkaro Najeriya

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, (NPA), ta sanar da cewar manyan jiragen ruwan guda ashirin da bakwai sun nufo Najeriya dauke da kayan abinci, tataccen man fetir da sauran kayayyaki zasu shigo Najeriya ta Legas.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito hukumar NPA ta sanar da haka ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Agusta, inda tace jiragen zasu fara shigowa Najeriya ne ta tashoshin Apapa da Tin Can Island daga ranar 17 zuwa 25 ga watan Agusta.

KU KARANTA: Kano ta dabo tumbin giwa: Buhari da Ganduje zasu samar da bahaya miliyan 20 a jihar Kano

Jiragen dankaro guda 27 cike da kayan abinci makil sun tunkaro Najeriya

Jirgin dankaro

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin kayayyakin da jiragen suka dauko akwai, jirage bakwai na dauke da tataccen man fetir, yayin da jirage ashirin ke dakon garin Fulawa, danyen kifi, masara, gishiri, kayan karafa da sauran sundukai.

Hukumar NPA tace a yanzu haka jirage guda goma sha hudu sun sauka a tashoshin jirgen suna jiran a sauke kayan da suka yi dakonsu daga kasashen waje zuwa Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel