Kotu ta bada belin ma'aikacin jaridar Premium Times

Kotu ta bada belin ma'aikacin jaridar Premium Times

Kotu ta saki wannan ma'aikacin jaridar ta Premium Times mai suna Samuel Ogundipe, wanda aka kama ranar Talatar nan data gabata

Kotu ta bada belin ma'aikacin jaridar Premium Times

Kotu ta bada belin ma'aikacin jaridar Premium Times

Kotu ta saki wannan ma'aikacin jaridar ta Premium Times mai suna Samuel Ogundipe, wanda aka kama ranar Talatar nan data gabata.

An saki Mr Ogundipe ranar juma'ar nan da safe, wanda alkalin kotun majistire ta Kubwa dake Abuja, Mai Shari'a Abdulwahab Mohammed ya ba da belin shi.

DUBA WANNAN: Wata mata ta bayyana yanda matsafan da suka sace ta suke amfani da jinin mutane wurin yin tsafe-tsafe

Alkalin kotun ya fara sauraron karar dan jaridar ranar Larabar da ta gabata, jim kadan bayan an kawo Mr Ogundipe, sannan a ranar ne alkalin kotun ya bukaci 'yan sanda da su rike shi har sai ranar 20 ga watan Disambar wannan shekarar.

Bayan haka yau da safen nan, jaridar PREMIUM TIMES ta samu labarin cewar za'a kara kai Mr Ogundipe wannan kotun, inda ba shiri lauyan kamfanin ya halarci kotun.

A kotun ne lauyan ya bukaci a bashi belin Mr Ogundipe, inda bai samu wata matsala ba sosai aka sake shi.

Alkalin Kotun shine ya bada belin na shi akan kudi naira 500,000, da kuma shaida wanda zai wakilce shi a kotu. A karshe kamfanin ya cika duk wasu sharuda da kotun ta gindaya, kuma an samu nasarar sakin Mr Ogundipe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel