Daruruwan mutane sun yi gangami a Jigawa domin marawa sanatan da ya koma PDP baya

Daruruwan mutane sun yi gangami a Jigawa domin marawa sanatan da ya koma PDP baya

Magoya bayan sanata Ubale Shitu sun karade unguwannin Jigawa kan sauya shekar da sanata mai wakiltan Jigawa ta arewa maso gabas yayi a kwannan nan.

Magoya bayan nasa sun kewaye unguwannin karamar hukumar Hadejia domin nuna biyayyarsu ga sanatan da ya sauya shekar.

Premium Times ta rahoto cewa koda dai Shitu bai kasance a wajen taron ba, uban tafiya a gangamin, Tijjani Usman, ya fadama ayarin jama’a cewa an shirya gangamin ne domin nuna goyon baya ga sanatan.

Daruruwan mutane sun yi gangami a Jigawa domin marawa sanatan da ya koma PDP baya

Daruruwan mutane sun yi gangami a Jigawa domin marawa sanatan da ya koma PDP baya

Usman yace Sanatan yayi biyayya ga mazabar kan kira da tayi na ya sauya sheka daga jam’iyyar Progressives Congress (APC) mai mulki.

KU KARANTA KUMA: Kyawawan hotunan iyalan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, matarsa da yaransa

Yace akwai bukatar sanatan ya sauya sheka saboda rashin aminci kan gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru wadda ya gaza cika alkawaran da ya daukarwa mutane.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel