Gwamnatin Buhari gwamnatin makaryatace – Inji Atiku

Gwamnatin Buhari gwamnatin makaryatace – Inji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana gwamnatin APC a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin gwamnatin makaryata, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Atiku ya bayyan haka ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta a yayin ziyarar daya kai jihar Enugu, inda aka jiyi shi yana cewa makaryata ne suka cika gwamnatin APC.

KU KARANTA: Buhari da Ganduje zasu samar da bahaya miliyan 20 a jihar Kano

Rahotanni sun bayyana cewar jami’an tsaro sun mamaye filin sauka da tashin jirage na jihar Enugu inda Atiku ya sauka, sa’annan suka cigaba da binsa duk inda zashi duk cewa mabiyansa sun yi cincirindo suna dakunsa.

Gwamnatin Buhari gwamnatin makaryatace – Inji Atiku

Atiku

Da yake gabatar da jawabi ga mabiyansa a ofishin jam’iyyar PDP na jihar, Atiku yace: “Gwamnatinnan gwamnatin makaryatace, sun yi alkawarin samar da ayyuka miliyan uku a duk shekara, sai gashi ana rasa ayyuka miliyan uku a duk shekara.”

Atikun yace sakamakon rasher ashen ayyuka da ake fama dashi a Najeriya ne ke janyo matsalolin tsari daban daban da suka addabi sassan kasar nan, inda yace shaidan na tasiri akan duk mutumin da bashi da aiki balle sana’a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel