Wata mata ta bayyana yanda matsafan da suka sace ta suke amfani da jinin mutane wurin yin tsafe-tsafe

Wata mata ta bayyana yanda matsafan da suka sace ta suke amfani da jinin mutane wurin yin tsafe-tsafe

- Wata mata ta tsallake rigiya da baya.

- A gabana suka harbe daya daga cikin matan da muke tare da ita

- Sun kira wani a waya suna shaida masa sun shirya masa sassan jikin

Wata mata ta bayyana yanda matsafan da suka sace ta suke amfani da jinin mutane wurin yin tsafe-tsafe

Wata mata ta bayyana yanda matsafan da suka sace ta suke amfani da jinin mutane wurin yin tsafe-tsafe

A ranar Lahadi ne 12 ga watan Augusta 2018 wata mata ta bayyana wa hukumar yan sanda yanda ta tsere daga hannun wasu mutane dake yanka mutane.

Matar mai suna Precious tace a farko da dauka masu garkuwa da mutane ne, amma daga baya suka kashe wata mata da aka sace su tare sannan suka kira wani daganan na fahimci masu yanka mutane ne.

DUBA WANNAN: Kuji dalilin da ya hana Serena Williams cin wasa kwallon tennis

Precious inda take magana da manema labarai a hukumar yan sanda a Port Harcourt tace taga mutane da dama wadanda suka hada da yara tace sunata rokon mutanen dasuji tausayin su karsu kashe su.

Tace bayan sun kashe matar sai suka kira wani wanda suka ambata da 'Alhaji' suka shaida masa cewa wasu sassan jikin sun samu.

Daga baya suka fahimci cewa masu yaki da masu garkuwa da mutane sun biyo sahun su zuwa cikin dajin sai suka ce mana su bamasu garkuwa da mutane bane masu saida sassan jikin dan adam ne.

Shigowar yan sanda dajin ne ya firgita su, sai suka kwashemu suka kaimu wani wajen daganan kuma fada ya kaure a tsakanin su, Precious tace tayi amfani da wannan dama ta tsere daga wajen su.

Precious ta shawarci yan sanda dasuyi kokarin mamaye dajin data tsiri don su ceto ragowar mutanen dake wajen.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel