An kai karar sanata kotu kan sauyin sheka, kotu ta aiko sammaci

An kai karar sanata kotu kan sauyin sheka, kotu ta aiko sammaci

Babban kotun tarayya da ke Abuja ta umurci Sanata Stella Oduah (APGA, Anambra) ta gurfana gabanta domin kare kanta daga karar da wani lauya mazaunin Abuja, John Mary Jideobi ta shigar game da ita.

Alkalin kotun, Ahmed Musa, ya bayar da wannan umurnin ne a ranar Talata bayan an shigar da karar inda ake nema kotu bawa jam'iyyar PDP ikon karbe kujerar Sanata Oduah sakamakon sauya sheka da tayi zuwa jam'iyyar APGA.

An kai karar sanata kotu kan sauyin sheka, kotu ta aiko sammaci

An kai karar sanata kotu kan sauyin sheka, kotu ta aiko sammaci

An zabe Mrs Oduah ne a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a shekarar 2015 amma tayi baran-baran da jam'iyyar bayan ta gaza samun tikitin takarar gwamna a zaben jihar Anambra da aka yi a shekarar 2017.

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

A bayanan da ya Premium Times ta samu, Mr Jideobi ya bukaci kotu ta tantance hallarcin kasancewar Mrs Oduah a kujerar ta na Sanata bayan ta fice daga jam'iyyar PDP ta koma APGA.

Kamar yadda lauyan ya bayyana a cikin takardan karar, ya dace wanda ake karar, Mrs Oduah tayi murabus daga kujerar ta bayan ta fice daga jam'iyyar aka zabe ta a karkashinta.

Wanda ya shigar da karar yana rokon kotu ta umurci Mrs Oduah tayi murabus daga kujerar ta.

Kotun ta bukaci wanda ake karar Sanata Stella Oduah ta gurfana a gabanta domin ta kare kanta daga karar da aka shigar game da ita.

Alkalin kotun ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 29 ga watan Augusta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel