Ministan cikin gida ya sanar da ranaku guda biyu domin hutun Sallah ga ma’aikata

Ministan cikin gida ya sanar da ranaku guda biyu domin hutun Sallah ga ma’aikata

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranakun Talata, 21 ga watan Agusta da Laraba, 22 ga watan Agusta a matsayin ranakun hutu ga ma’aikata musamman Musulmai don gudanar da bukukuwan Sallah babba na shekarar 2018, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta, cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar cikin gida Mohammed Umar ya fitar.

KU KARANTA: Mai martaba Sarkin Daura ya nada Orji Uzor Kalu wata babbar sarauta a masarautar Daura

Dambazau ya yi fatan Allah yasa ayi shagulgulan Sallah lafiya, sa’annan yayi kira ga jama’an kasa dasu yi amfani da wannan dama don nuna ma juna soyayya da kuma kaunar juna, don cigaban kasar nan gaba daya.

Ministan cikin gida ya sanar da ranaku guda biyu domin hutun Sallah ga ma’aikata

Sallar Idi

Daga karshe Dambazau yayi kira ga yan Najeriya dake ciki da wajen kasarnan dasu baiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon bayan don tabbatar da burin gwamnatin na hadin kan yan kasa da samar da cigaba mai daurewa.

A wani labarin kuma mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya sanar da ranar Talata, 21 ga watan Agusta a matsayin ranar da Musulman Najeriya zasu gabatar da bikin babbar Sallah.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel