2019: Atiku ya yi alfahari da kwarewar sa a warware wata matasalar da ya ce tafi damun Najeriya

2019: Atiku ya yi alfahari da kwarewar sa a warware wata matasalar da ya ce tafi damun Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya jaddada bukatar gaggauta magance matsalar rashin aikin yi a kasar nan domin kiyaye matsalar da hakan zata jawo a gaba.

Atiku ya bayyana haka ne yau, Alhamis, a Enugu a cigaba da ziyarar tuntuba da yake yi domin neman goyon baya a takarsa ta shugaban kasa.

A cewar sa, matsalar rashin aikin yi a Najeriya abin damuwa ne tare da bayyana cewar akwai bukatar ta dauki wannan matsala da muhimmanci. Atiku ya ce kimanin mutane miliyan 12 sun rasa aikinsu tare da bayyana cewar wasu masu aikin ma ya kamata a ce suna aikin da yafi wanda suke yi.

2019: Atiku ya yi alfahari da kwarewar sa a warware wata matasalar da ya ce tafi damun Najeriya

Atiku

A kalamansa: “A yau muna fuskantar matsalar rashin aikin yi mafi muni a tarihin Najeriya wacce ta haifar da matsala ga tsaron kasa.”

DUBA WANNAN: Yaki da cin hanci: Hukumar 'yan sanda tayi babban kamu a jihar Kano

Na kware a bangaren samar da aikin yi, hakan ya saka lokacin da muke gwamnati aka samu raguwar rashin aikin yi da kasha 7%. Abinda Najeriya tafi bukata shine mutumin da zai samar da aiyuka ga matasa da ma kowa da kowa, kuma nine nake da wannan kwarewa,” a cewar Atiku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel