Gwamnatin Tarayya ta biya Maƙudan Kuɗi na Fansar 'Yan Matan Dapchi

Gwamnatin Tarayya ta biya Maƙudan Kuɗi na Fansar 'Yan Matan Dapchi

Majalisar Dinkin duniya ta bayyana cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta biya makudan kudi na fansar 'yan Matan Dapchi da 'yan ta'adda na Boko Haram su kayi garkuwa da su a watan Maris na shekarar 2018 da ya gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, a baya gwamnatin Najeriya ta musanta rahoton cewa ta biya miliyoyin dukiya wajen fansar 'yan Matan Dapchi, inda ta ce ta fanshe su ta hanyar musaya da kwamandun 'yan Boko Haram dake tsare a hannun hukumomin kasar nan.

Sai dai binciken Majalisar dinkin duniya ya tabbatar da cewa, kudin fansar garkuwa, gudunmawa daga kungiyoyin agaji da kuma tattalin arzikin kuɗi ke ci gaba da tallafawa gudanar al'amurran 'yan ta'addan na Boko Haram da sauran kungiyoyin ta'adda a yankin Tafkin Chadi.

Gwamnatin Tarayya ya biya Maƙudan Kuɗi na Fansar 'Yan Matan Dapchi

Gwamnatin Tarayya ya biya Maƙudan Kuɗi na Fansar 'Yan Matan Dapchi

Majalisar ta bayyana hakan ne da sanadin wani bincike karo na 22 da aka gudanar kan al'amurran da suka shafi alakar dake tsakanin kungiyar ta'adda musamman ta ISIS da wasu kungiyoyi.

KARANTA KUMA: Jakadan Najeriya ya yabawa Shugaba Buhari kan sabuwar Doka mai baiwa Matasa dama a harkokin Siyasa

Binciken ya tabbatar da cewa, akwai wani adadi na kungiyoyi masu zaman kansu dake bayar da gundunmuwar kudi ga kungiyoyin ta'adda domin samun dama ta ci gaba da cin Karen su ba bu babbaka a yankin Hamada na Afirka.

Legit.ng ta fahimci cewa, a ranar 18 ga Fabrairun da ta gabata ne 'yan ta'adda na Boko Haram suka yi garkuwa da 'daliban makarantar Dapchi 111 inda gwamnatin tarayya ta karbi fansar su da makudan kudi kamar yadda binciken majalisar dinkin duniya ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel