Karin Albashi: Gwamnonin Najeriya sun fara kwalo-kwalo

Karin Albashi: Gwamnonin Najeriya sun fara kwalo-kwalo

- Gwamnonin Najeriya sun bayyana takaicinsu bisa yadda aka takaita aikin gwamnatoci ga biyan albashi kawai ba tare da la’akari da ragowar bangarori ba

- Shugaban kungiyar gwamnoni Najeriya, Abdulaziz Yari, ya bayyana cewar gwamnonin Najeriya ba zasu iya biyan N65,000 a matsayin mafi karancin albashi kamar yadda kungiyar kwadago (NLC) k enema ba

- Zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya caccaki gwamna mai baring ado, Ayo Fayose, bisa daukan sabbin malaman makaranta watanni biyu kafin ya bar Ofis

Gwamnonin Najeriya sun bayyana cewar ba an zabe su don biyan albashi bane kawai tare da bayyana cewar akwai wasu aiyukan kamar gina ingantattun hanyoyi, samar da wutar lantarki, da ilimi da ragowarsu dake bukatar a basu kulawa.

Karin Albashi: Gwamnonin Najeriya sun fara kwalo-kwalo

Abdulaziz Yari

Gwamnonin sun bayyana hakan ne a kungiyance gabanin bayyana sabon Karin albashi da gwamnatin tarayya ke shirin yi a watan Satumba.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulaziz Yari, ya bayyana cewar abin takaici ne yadda aka mayar da aikin gwamnoni kawai su biya albashi ba tare da jama’a na la’akari da ragowar aiyukan dake wuyan gwamnonin ba.

DUBA WANNANN: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu don taya musulmi murnar sallah

Kazalika ya bayyana cewar gwamnonin ba zasu iya biyan N65,000 a matsayin mafi karancin albashi ba kamar yadda kungiyar kwadado(NLC) ke bukata ba.

A wani labarin mai alaka da wannan, zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya soki gwamna mai baring ado, Ayo Fayose, da yunkurin haifar mnasa da cikasa a mulkinsa ta hanyar daukan malaman makaranta masu dumbin yawa yayin day a rage masa kasa da watanni biyu ya bar ofis.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel