Babbar Magana: Kotu ta yiwa babban sufetan ‘yan sanda albishir da tura shi gidan yari

Babbar Magana: Kotu ta yiwa babban sufetan ‘yan sanda albishir da tura shi gidan yari

Wata babbar kotu dake zamanta a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, karkashin mai shari’a, Ibrahim Yusuf, tayi barazanar tisa keyar babban sifetan hukumar ,yan sandan Najeriya, Idris Ibrahim, zuwa gidan yari saboda raina umarninta.

Kotun na zargin Idris da raina umarninta na sakin Mista Olalekan Alabi, wani mataimaki na musamman a kan harkokin siyasa ga gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed.

Barazanbar tura Sufeto Idris gidan yarin na kunshe ne cikin wata takardar jan kunne mai lamba ta 48 da kotun ta buga a ranar 10 ga watan Agusta.

Takardar da aka raba ga manema labarai yau, Alhamis, a Ilorin ga manema labarai na dauke da saka hannun rajistaran kotun.

Babbar Magana: Kotu ta yiwa babban sufetan ‘yan sanda albishir da tura shi gidan yari

Babban sufetan ‘yan sanda, Ibrahim Idris

A cikin takardar, a lkalin kotun, Yusuf, ya ce “ka sani cewar matukar baka yi biyayya ga umarnin babbar kotu dake jihar Kwara ba a kan hukuncin da ta yanke ranar 1 ga watan Agusta, 2018, ba tamkar nuna raini ga bangaren shari’a ne wanda hukuncinsa shine tisa keyar ka zuwa gidan yari.”

DUBA WANNAN: Ana kukan targade: PDP ta kara rasa 'yan majalisa 5

Hukumar ‘yan sanda ta kama tare da tsare Alabi ne tun ranar 30 ga watan Mayu bayan an yi zarginsa da alaka mai karfi da ‘yan fashin garin Offa.

Sai dai mai shari’a Yusuf ya bayar da umarnin a saki Alabi a kan beli na wucin gadi a ranar 1 ga watan Agusta tare da bayyana cewar babu hujjar cigaba da tsare shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel