Shugabannin hukumomin tsaro sun amsa kiran Osinbajo

Shugabannin hukumomin tsaro sun amsa kiran Osinbajo

Shugabanin hafsoshin sojin Najeriya suna daga cikin wadanda suka hallarci taron majalisar zartarwa na kasa NEC wanda ake gudanarwa yanzu a fadar Aso Villa karkashin jagorancin mukadashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo.

Shugabannin hukumomin tsaro sun amsa kiran Osinbajo

Shugabannin hukumomin tsaro sun amsa kiran Osinbajo

Cikin wadanda suka hallarci taron sun hada da Shugaban hafsin sojin kasa, Laftanat Tukur Buratai, Shugaban hafsin sojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas, Shugaban sojin sama, Ahmed Abubakar Sadique, Direktan Hukumar Binciken Sirri na kasa (NIA), da Sufeta Janar na 'Yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris.

DUBA WANNAN: Kayi tsufa da mulkin Najeriya - Tambuwal ya fadawa Buhari

Sauran wadanda suka hallarci taron sun hada da gwamnoni jihohi, ministoci da shugabanin wasu hukumomin gwamnati.

A wata rohoton, Legit.ng ruwaito cewa Al-Mustapha tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha ya ce a shirye yake ya fito takarar shugabancin kasa a shekarar 2019 muddin jama'a sun bukaci ya fito.

Manjo Al-Mustapha (murabus) ya yi bayyana haka ne a jiya Laraba a wata hira da ya yi da manema labarai a Kaduna jim kadan bayan ya kammala taro da 'yan kungiyar United Christian Leaders Eagle Eye Forum da suka nemi ya fito takarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel