Saraki ya dade yana renon kudirin takarar shugaban kasa tun 2011 – Baraje

Saraki ya dade yana renon kudirin takarar shugaban kasa tun 2011 – Baraje

Tsohon shugaban kungiyar sabuwar APC, Alhaji Kawu Baraje ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa ya dade da kaddamar da kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa, cewa kuma hakan ba laifi bane.

Da yake magana da manema a Ilorin a ranar Alhamis wajen yaye dalibai na makarantar Islamiya, Alhaji Baraje, ya bayyana cewa Saraki na kokarin gwada sa’arsa na zama shugaban kasar tun a 2011.

Saraki ya dade yana renon kudirin takarar shugaban kasa tun 2011 – Baraje

Saraki ya dade yana renon kudirin takarar shugaban kasa tun 2011 – Baraje

Da yake magana akan yunkurin tsige Saraki, Baraje yayi korafin cewa kaso biyu cikin uku na sanatoci 109 ne kadai zasu iya aiwatar da tsigewar, ba wai kaso biyu cikin uku dake wajen da za’a tsige shi ba.

KU KARANTA KUMA: An nada jarumi Ali Nuhu jakadan yaki da shan miyagun kwayoyi

Alhaji Baraje ya kuma bayyana cewa nan da yan kwanaki zai komawa tsohuwar jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP) tare da magoya bayansa kamar yadda ya kamata doka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel