Koda PDP ce ta samu nasara a 2019 zamu yarda – Osinbajo

Koda PDP ce ta samu nasara a 2019 zamu yarda – Osinbajo

- Yayin da hadarin zabe ke kara haduwa a Najeriya, gwamnati mai ci ta ayyana kudirinta na gudanar da sahihin zabe

- Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya furta hakan yayin wani taro

Mukadashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari zata yi duk mai yiwuwa don ganin an yi sahihin zabe a shekara ta 2019.

Koda PDP ce ta samu nasara a 2019 zamu yarda – Osinbajo

Koda PDP ce ta samu nasara a 2019 zamu yarda – Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasar ya samu wakilci ne a taron da jam'iyyun kasar nan ke shiryawa duk shekara, wanda Babafemi Ojodu mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin siyasa ya wakilci shi a taron.

Ya ce dukkanin wasu shirye-shirye da za a yi domin tunkarar zaben ana cigaba da yin su, kuma ana sa ran kowacce jam'iyyar siyasa zata bada hadin kai domin aiwatar da sahihin zabe.

KU KARANTA: Da duminsa: Obasanjo da DanKwambo sun sanya labule

Ya ce "Cigaban Najeriya sama yake da bukatar kowane dan siyasa ko jam'iyya. Hakkinmu ne mu kare dukkan wani dan Najeriya ta hanyar gudanar da sahihin zabe"

"Ya kamata mu yi duk abinda ya kamata wajen ganin an hana kowa yin amfani da munanan kalamai ko dabi'un da zasu iya jawo rikici a yayin zabe".

"Wannan taro zai bawa jam'iyyu damar tattaunawa da juna. Saboda rashin fahimtar juna da sauran matsaloli".

"Nayi alkawari cewa zamu yi dukkan mai yiwuwa domin ganin an cimma nasara a zabe mai zuwa. Zamu taimaki hukumar zabe da duk abinda take bukata domin gudanar da zaben yadda ya kamata.

Haka zalika ne kowacce jam'iyya ta bi dokar zabe dan samun tabbataccen zaman lafiya ". Wakilin mukaddashin shugaban kasar ya jaddada.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel