Wani dan Najeriya ya kwashi 'yan kallo a wani jami'ar kasar turai

Wani dan Najeriya ya kwashi 'yan kallo a wani jami'ar kasar turai

Wata babbar jami'ar kasa-da-kasa dake a kasar Amurka ta karrama wani hazikin dan Najeriya mai suna Prince Onyeka Nnadozie da digirin digirgir a fannin kimiyya da kuma iya mulkin jama'a.

Shi dai Prince Onyeka Nnadozie kamar yadda muka samu shine shigaban gidauniyar Prince Osisioma da ta shahara wajen tallafawa gajiyayyu da masu karamin karfi musamman ma ta fannin ilimi a tarayyar Najeriya.

Wani dan Najeriya ya kwashi 'yan kallo a wani jami'ar kasar turai

Wani dan Najeriya ya kwashi 'yan kallo a wani jami'ar kasar turai

KU KARANTA: An kama wasu masoya suna badala a bainar jama'a a Saudiyya

Legit.ng ta samu cewa mahukuntan jami'ar dai sun ce sun yanke shawarar karrama Prince Onyeka Nnadozie din saboda yadda suka ga yana taimakon al'umma ba dare ba rana.

Da yake mayar da jawabi a yayin karramawar, shima dai ya bayyana jin dadin sa game da karramawar sannan kuma ya sha alwashin cigaba da yin ayyukan alherin na sa.

A wani labarin kuma, Tsohon Gwamnan jihar Jigawa dake a arewacin Najeriya kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), watau Alhaji Sule Lamido ya ce yaki da cin hanci da rashawar da Buhari yake yi babu gaskiya a cikin sa.

Alhaji Sule Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a garin Lokoja babban birnin jihar Kogi a cigaba da zagayawa rangadin gaisuwa da musabaha da yakeyi da jiga-jigan jam'iyyar PDP game da zaben sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel