Karanta dalilin 'yan sanda na bincikar wakilin jaridar PremiumTimes

Karanta dalilin 'yan sanda na bincikar wakilin jaridar PremiumTimes

- Tsare 'yan jarida a kasashe masu tasowa ba abu ne sabo ba, walau sunyi laifi ko akasin haka

- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi karin haske kan yadda suke cigaba da tsare wani dan jarida saboda wallafa wani rahoto

- Inda suke takura shi dole ya bayyana yadda akai ya samo zaran da ya saka labarinsa, wanda yin hakan gingimemen zunubi ne a dokar aikin jarida

A ranar Alhamis din nan ne rundunar 'yan sandan ta fitar da sanarwa akan kamen da ta yiwa Samuel Ogundipe bisa zargin sata, da mallakar bayanai ta haramtacciyar hanyar abinda ka iya zamowa barazana ga tsaron kasa gami da haifar da tashin hankali.

Karanta dalilin 'yan sanda na bincikar wakilin jaridar PremiumTimes

Karanta dalilin 'yan sanda na bincikar wakilin jaridar PremiumTimes

Sanarwar da kakakin rundunar DCP Jimoh Moshood ya sanyawa hannu ta ce tuni aka gurfanar da dan jaridar a gaban kotu, bisa tuhumar saba dokar kiyaye sirrin gwamnati, da laifukan da suka shafi kafofin internet.

Tun da farko dai rundunar 'yan sandan dai sun bukaci ala tilas Ogundipe ya bayyana inda ya samo labarinsa, wanda yin haka ya sabawa ka'idar aikin jarida.

KU KARANTA: ‘Yan sanda sun yi namijin kokorin kama ‘yan bindiga 20 da makamai masu yawa a Zamfara

To sai dai tuni kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International da sauran kungiyoyi suka yi tir da abinda suka kira tauye 'yanci albarkancin baki da matsi ga 'yancin aikin jarida a kasar nan.

Idan za'a iya tunawa dai dan jaridar ya wallafa wata wasikar da ake zarginsa da kwarmatawa da ta kunshi tsame hannun 'yan sanda kan hana wasu sanatoci shiga majalisar tarayya dake Abuja.

Wasikar mai shafi biyar ta ambato Sufeto Janar na 'yan sandan kasar yana yiwa mukaddashin shugaban kasa karin bayani kan tsare tsohon shugaban DSS Lawal Daura, da binciken da ake gudanarwa a kansa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel