Amarya ta watsa wa kishiyarta da jaririnta tafashasshiyar miya

Amarya ta watsa wa kishiyarta da jaririnta tafashasshiyar miya

Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta kama wata amarya wadda ta watsa wa uwargidanta tare da danta mai watanni 10 a duniya tafashasshiyar miyar kubewa a jikinsu.

Kakakin 'yan sandan jihar, CP Abdu Jinjiri ya tabbatar da akuwar lamarin a garin Gantsa da ke karamar hukumar Buji ta jihar.

An tattaro cewa jajririn ya rasa ransa a sanadiyyar faruwar lamarin.

Hakan ya samo asali ne sakamakon sabanin da ya shiga tsakanin abokan zaman guda biyu.

Amarya ta watsa wa kishiyarta da jaririnta tafashasshiyar miya

Amarya ta watsa wa kishiyarta da jaririnta tafashasshiyar miya

Amaryar wadda ba ta wuce shekara 20 da haihuwa ba tana dakin girki ne a lokacin da uwargidan, rungume da danta, ta shiga dakin dafa abincin, daga nan, sai amaryar ta fara mayar mata da magana.

Daga nan sai cacar baki ta kaure. Ba tare da bata lokaci sai ita kuma amaryar ta dauki tukunyar miya tana tafarfasa ta watsa wa uwargidan da danta a jikinsu.

Bayan ta watsa musu miyar ne sai amaryar ta fara ihu tana neman a kawo musu taimako.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce uwargidan tana babban asibItin Dutse tana karbar magani, kuma duk jikinta ya daye, amma yaron ya rasu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An nada Nnochirionye Afunanya a matsayin sabon kakakin hukumar DSS

Kwamshinan 'yan sandan jihar CP Bala ya bayar da umarnin a kai amaryar da ta aikata lamarin sashen binciken kwakwaf domin gudanar da bincike da kuma yi mata hukuncin da ya dace.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel