Zaben shugabancin kasa na 2019: Saraki na nazari ne bai kaddamar ba – Hadiminsa

Zaben shugabancin kasa na 2019: Saraki na nazari ne bai kaddamar ba – Hadiminsa

Hadimi na musamman ga Sanata Bukola Saraki akan shafukan zumunta na zamani, Olu W. Onemola ya fayyace gaskiya akan matsayar shugaban majalisar dattawan na tsayawa takara shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zabe mai zuwa.

Ku tuna cewa a wata ganawa da akayi da Saraki wanda aka wallafa a Bloomberg a ranar Laraba, 15 ga watan Agusta yace yana nazari akan tsayawa takara da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Tattaunawar ya haddasa kace-ce daga wasu yan Najeriya dake ganin cewa shugaban majalisar dattawar ya kaddamar da kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa a fakaice.

Zaben shugabancin kasa na 2019: Saraki na nazari ne bai kaddamar ba – Hadiminsa

Zaben shugabancin kasa na 2019: Saraki na nazari ne bai kaddamar ba – Hadiminsa

Don haka, Onemola yace Saraki bai kaddamar da kudirinsa na takarar shugabancin kasa ba.

KU KARANTA KUMA: Daga Buhari har Lalong zasu kai labari a 2019 – Kakakin majalisar dokokin jihar Plateau

Cewa abunda Saraki ya fadi ba sabon abu bane cewa mafi akasarin maganarsa ya karkata ne ga tattalin arziki ba wai siyasa ba, cewa kamar koda yaushe masu kawo rahoto sun dauki lamarin ta sigar su ne.

Cewa lokaci na nan zuwa da yan Najeriya zasu san shirinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel